Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Republican Sun Fitar da Rahoton Binciken Harin da Aka Kai Benghazi


Paul Ryan, kakakin majalisar wailan Amurka, majalisar da ta nace kan binciken harin Benghazi
Paul Ryan, kakakin majalisar wailan Amurka, majalisar da ta nace kan binciken harin Benghazi

'Yan jam'iyyar Republican dake da rinjaye a majalisun wakilai da na dattawan Amurka sun fitar da rahoto akan harin da aka kai ofishin jakadancin Amurka a Benghazi dake kasar Libya, harin da yayi sanadiyar mutuwar jami'an diflomasiyar Amurka hudu

Wani binciken da jamiyyar Republican take jagoranta game da harin ta'adancin da aka kai a ofishin jakadancin Amurrka dake Benghazi na kasar Libya cikin shekarar 2012, wanda yayi dalilin mutuwar Amurkawa 4 an kawo karshen sa a jiya Talata, ba tare da samun wani sabon madogara ba akan rawar da tsohuwar sakatariyar harkokin wajen na wannan lokacin Hilary Clinton ta dauka da cewa ya saba.

Hillary ta bi sawun wannan binciken sau da kafa.

A 11 ga watan Satumbar shekarar 2012 ta fada a wajen yakin neman zabenta cewa kwamitin bincike na majilisar wakilai bai samu wata hujja ba da zai harfar da wani rudani ba har da za'a iya dora mata wani laifi.

Hillary tace don haka yanzu lokaci yayi da zamu ci gaba.

Sai dai da yawan ‘yan jamiyyar ta Republican dake cikin tawagar wannan binciken sunce laifin rundunar sojan kasar ce da suka ki daukar matakin da ya dace nan da nan a lokacin da wannan abu ya faru.

Shugaban tawagar binciken dan majalisa Trey Goowdy yace ba wani sojan Amurka da aka tura a Benghazi duk ko da umurnin da shugaba Barrack Obama ya bayar, shi da sakataren harkokin tsaro na wannan lokacin Leon Panetta

XS
SM
MD
LG