Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MSF Ta Ce Akwai Bukatar Gagarumin Aikin Gaggawa Na Jinkai A Arewa Maso Gabashin Najeriya


Kungiyar agajin ta likitoci ta ce akwai bukatar gaggawa ta taimakawa mutane su akalla dubu 500 dake fuskantar tsananin karancin abinci, magunguna, ruwan sha da mafaka.

Kungiyar agaji ta likitoci da ake kira "Médecins Sans Frontières" ko MSF a takaice, ta yi kiran da a kai daukin gaggawa ga mummunan bala'in jinkai da ake fuskanta a Jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, inda mutane akalla dubu 500 suke cikin tsananin karancin abinci, magunguna, ruwan sha da kuma matsuguni.

Darektar gudanar da ayyuka ta kungiyar MSF, Dr. Isabelle Defourny, ta ce "tilas kungiyoyin bayarda agaji su kaddamar da gagarumin aikin jinkai domin tinkarar wannan lamarin."

A yayin da sojojin Najeriya suke ci gaba da kwato garuruwa da kauyuka daga hannun 'yan Boko Haram, duniya tana kara ganin irin mummunar matsalar jinkai da aka shiga a wannan yankin in ji kungiyar.

Wasu daga cikin mutanen sun shafe shekara har biyu ba su iya hulda da kowa a waje. 'Yan gudun hijirar dake zaune yanzu haka a garuruwan da sojoji suka kwato, sun dogara ne kacokam a kan agaji daga waje, yayin da wasunsu suka kamu da cutar rashin wadatar abinci a jiki.

A watan da ya shige, wasu likitoci na kungiyar agajin sun gano wasu yara 16 dake dab da mutuwa saboda rashin abinci a wani sansanin 'yan gudun hijira dake garin Bama a Jihar Borno, wadanda tilas aka garzaya da su wani wurin ciyarwar gaggawa ta hanyar karin ruwa.

Kungiyar MSF ta ce hukumomi sun kwashe mutane kusan dubu 1 da 500 wadanda suka fi fama da yunwa da rashin lafiya, aka kuma kara yawan agajin abincin da ake ba sansanin. Amma kashi 15 cikin 100 na yaran dake wannan sansani su na fama da cutar yunwa mai tsanani, kuma mutane 40 suka mutu a cikin makonni ukun da suka shige.

Kungiyar MSF ta ce a bayan garin na Bama, akwaiu garuruwa kamar Monguno wanda shi ma yana da 'yan gudun hijira kimanin dubu 65 masu bukatar agaji, wadanda su ma tun watan Janairun shekarar 2015 ba su da magunguna.

XS
SM
MD
LG