Jakada Macharia Kamau ya shaidawa manema labarai cewar binciken da MDD ta yi don ta binciki lamarin na ranar 8 zuwa 11 ga watan Yuli, an dai yi ne kawai, amma daman an riga an san manufar da ake son a cimma.
Wata hukumar binciken mai zaman kanta da babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya kafa ta dora laifi ne a kan rashin ingantaccen shugabanci a bangaren manyan hafsoshin sojin zaman lafiyar, wanda hakan ne kuma ya yi sanadiyar barkewar fadar da ya janyo har aka kashe mutane kamar 300 a kasar.
A ranar Talata ne MDD ta bada sanarwar cewa a sakamakon bincikenda aka gudanar, ta yanke shawarar gaggauta maye gurbin babban komandan sojojin kiyayen zaman lafiyar , babban hafsin sojan Kenya Lieutenant General Johnson Mogoa Kimani Ondieki