Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malaysiya Zata Taimaka Wajen Ceto Rayuka A Somaliya


Dakarun Malaysiya
Dakarun Malaysiya

Jami’an Gwamnatin da na diflomasiyya na Somaliya sun fada a yau asabar cewa Kasar Malasiya zata tura dakaru zuwa Somaliya, a wani shiri na taimakon Al’umma da kuma yunkurin kawarda afkuwar bala’in yunwa da ceton rayukan dubban mutane.

Ministan yada labarai na Somaliya, Mohammed Abdi Hayir Mareye, gaskanta wannan labarin a tattraunawa da shahen Somali na VOA yana mai cewa, "Za mu bada cikakken bayani idan wakilan da suka kai ziyara Malaysia karkashin jagorancin Mataimakin Firaminista Mohamed Omar Arte, sun dawo .”

A lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Kuala Lumpur, Ministan Tsaron Malaysiya Datuk Seri Hisammuddin yace Kasar sa zata tura Hafsoshi uku da wasu Sojoji goma sha bakwai na rundunar kiwon lafiya ta Sojin kasar zuwa Somaliya.

Ministan ya kara da cewa wasu Sojojin kasa su goma sha daya da suka hada da Hafsa daya da Sojoji goma zasu zasu samarda tsaro ga wannan tawagar Sojoji a Somaliya. Abincin da kuma kayan magungunan za’a kai su Somaliya ne ta Jirgin Sama Kirar C-130 wanda ake wa lakabi da Hercules.”

Ministan yayi bayanin dakarun da kuma kayan za’a tattara su ne daga Riyadh, Saudi Arabia, inda suke da mazauni na Sojoji marasa yawa domin taimakawa wajen kwashe Yan kasar Malaysiya dake Yemen. Amma da yawa suna ganin wani bangare ne na Sojojin kawance don a yaki tsagerun Houthi a Yemen.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG