Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta Ya Nemi Gafara


Uhuru Kenyatta

Za a gudanar da zaben tsayar da 'yan takara ranakun litinin da talata a kasar Kenya

A kasar Kenya, shugaban kasar Uhuru Kenyatta ya nemi gafarar 'yan kasar sa a saboda soke zaben tsayar da 'yan takara da aka yi a ranar Juma’a bayan da mutane suka fito da yawan da ba’a zata ba.

Jiya Asabar shugaba Kenyatta ya ce gobe Litinin da ranar Talata idan Allah ya kaimu jam’iyar sa ta Jubilee zata gudanar da sabon zaben tsayar da 'yan takara da aka soke a gundumomi goma sha biyar daga cikin ashirin da daya a ranar Juma’a.

Ya fada a wata sanarwar daya gabatar cewa ba kasafai zaben tsayar da 'yan takara ke samun fitowar jama’a da dama kamar yadda aka gani a ranar Juma’a ba. Matsalolin da aka fuskanta sun hada harda rashin isassun kayayakin zabe da kura kurai da kuma rudami.

Ana gudanar da zaben tsayar da 'yan takarar ne kafin zaben da za’a gudanar a watan Augusta idan Allah ya kaimu, ciki harda na shugaban kasa.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG