Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Wargaza Shirin Kai Harin Ta'addanci Kan Masallacin Qa'abah


Mahajjata a lokacin aikin Hajji a Masallacin Qa'abah.

An kashe mutumin da yayi niyyar kai harin bam na kunar bakin wake a Masjidil Haram a lokacin da 'yan sandan suka rutsa shi a cikin gidansa, aka yi musanyar wuta, ya kuma tayar da bam ya kashe kansa ya rusa wannan gida.

‘Yan sanda a Sa’udiyya sun tarwatsa wata makarkashiyar da aka kulla ta kai hari a kan Masjidil Haram, a jiya jumma’a, suka kashe mutumin da yayi niyyar kai wannan harin lokacin da suka rutsa da shi a cikin gidansa.

Hotunan bidiyon da aka yada ta gidan telebijin na Sa’udiyya sun nuna ‘yan sanda a lokacin da suka kai farmaki kan gida mai hawa uku inda wannan dan niyyar kai harin kunar bakin wake ya zauna. ‘Yan sanda suka ce sun yi musanyar wuta da mutumin kafin ya tarwatsa kansa, abinda ya sa gidan ma baki dayansa ya rushe.

Ma’aikatar harkokin cikin gidan Sa’udiyya ta ce dan kunar bakin waken ne kadai ya mutu a tashin bam din. Ma’aikatar ta ce ‘yan sanda 5 da fararen hula 6 sun ji rauni.

An kama wasu mutane biyar, cikinsu har da mace daya, dangane da wannan makarkashiyar kai hari kan Masallacin na Qa’aba. Ma’aikatar ba ta ce ga kungiyar da ta shirya kai harin ba.

Iran da kuma kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon sun yi Allah wadarai da wannan kullalliyar ta kai hari a Masjidil Haram, wuri mafi tsarki ga Musulmi.

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bada sanarwa yau asabar inda ta ambaci kakakinta, Bahram Ghasemi, yana fadin cewa “ta’addanci ya zamo ruwan dare kuma yana yaduwa a duk fadin duniya.”

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG