Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Allah Wadai da Kisan da Aka Yiwa Wata 'Yar Jarida a Kasar Malta


Motar Daphne Caruana Galizia da bom ya tarwatsa
Motar Daphne Caruana Galizia da bom ya tarwatsa

Daphne Galizia wadda aka kashe a kasar Malta tana binciken wata badakalar cin hanci da rashawa ne a gwamnatin kasar

Cikin kakkausan lafazi, Amurka ta yi Allah wadai da kisan da aka yi wa wata ‘yar jarida mai suna Daphne Galizia, wacce ke binciken wata badakalar cin hanci da rashawa a gwamnatin kasar Malta.

“Wannan hari raggwanci ne, wanda ya dauki ran hazika kuma jarumar ‘yar jarida, wacce ta sadaukar da rayuwarta wajen tabbatar da bin doka da oda da kuma bankado cin hanci da rashawa,” Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Heather Nauert ta fada a jiya Talata.

Ta kuma kara da cewa hukumar bincike manyan laifuka ta FBI ta amsa gayyatar da Firai ministan kasar ya yi mata, na neman taimakon Amurka a binciken kisan.

Baya ga haka, akwai kwararru masu binciken kwakwaf ‘yan kasar Holland da suka isa kasar ta Malta domin taimakawa.

Wani harin bam da aka kai a ranar Litinin, ya tarwatsa motar Galizia, jim kadan bayan da ta bar gidanta, lamarin da ya sa motar ta kama da wuta ta kuma saki hanya ta fada wai fili.

Dan Galizia yana kallo motar mahaifiyarsa ta fashe, amma babu abinda zai iya yi domin ya ceceta.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG