Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Kunar Bakin Wake A Afghanistan Ya Halaka Mutane 6 Yau Lahadi


Wani dan kunar bakin wake ya halaka mutane 6 kana wasu 13 sun samu rauni a Afghanistan sai dai ba wanda ya dauki alhakin aikata wannan danyen aikin.

Wani dan kunar bakin wake ya hallaka fararen hulla 6 a gabashin Afghanistan a yau lahadi, kana wasu 13 sun samu rauni iri daban-daban.

Shi dai wannan dan kunar bakin waken yana bisa mashin ne kuma ya dunfari wurin da ake gangamin nuna goyon bayan gwamnati a Jalalabad fadar gundumar Nangahar.

Sailin da jamiaan tsaro suka ganshi sai suka hana shi kaiwa ga wurin taron, abinda yasa ya tada bomb din dake jikin sa har yayi wannan taadin.

Mai Magana da yawun Gwamnati a lardin Attaullah Khogyani ya tabbatar wa wanna gidan radiyon da wannan labarin , yace wata mata da danta na cikin wadanda wannan balain ya rutsa dasu.

Sai dai kawo yanzu ba wani wanda ya dauki alhakin aikata wannan aika-aikan.

Wannan dai yana faruwa ne kwana daya bayan da wani dan kunar bakin waken ya kashe wasu jamiaan tsaron kasar ta Afghanistan a Jalalabad kana wasu 10 suka samu rauni, sai dai s wannan kungiyar ISIS ta dauki alhakin aikata shi.

A jiya ne dai shugaba Ashraf Ghani yace kungiyar ta IS tana cikin halin dar-dar domin ko gwamnatin Afghanistan ta matsa kaimi wajen ganin ta fatattake ta.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG