Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bature Na Farko Cikin Turawan Da Aka Kwace Ma Gonaki, Ya Koma Gonarsa A Zimbabwe


Darryn Smart dan Robert Smart sanda ake karbar su a gonarsu
Darryn Smart dan Robert Smart sanda ake karbar su a gonarsu

An samu nasarar maidawa daya daga cikin turawan da aka kwace musu gonaki a gwamnatin Shugaba Robert Mugabe gonar shi kuma mutanen garin sunyio murna da hakan sosai.

Daya daga cikin turawan manoman da gwamnatin Shugaba Robert Mugabe mai murabus ta kora daga gonakinsu, ya zama bature manomi na farko da ya samu sukunin komawa gonarshi.

sojoji sun raka Robert Smat zuwa gonarsa dake Lesbury, mai tazarar kilomita 200 a gabas da Harare, babban birnin kasar a jiya alhamis. An ajiye wani soja cikin motarsa, a kofar gonar ko da Smart zai bukace shi. Smart bai bukaci taimakon sojan ba.

Ma'aikatan gonar bakaken fata sun yi ta guda, wasu na zub da hawaye a lokacin da suke tarbar Smart da iyalansa. Ma'aikatan sun yi shekaru aru aru suna aiki a wannan gona, kafin su ma a kore su a lokacin da aka kori Smart.

Lokacin mulkin turawan kasar, turawa sun kampaci gonakin da suka fi kowanne albarka a kasar inda suka bar bakake a inda ba sosai ke da kyau ba.

Mugabe yace korar turawan da akayi wani yunkuri ne na duba bangarancin da ke akwai akan harkar gonakin da ba'ayi wa bakake adalci ba kuma yake taimakawa turawan da basu kai kaso daya cikin darin mutanen garin ba.

Mallakar filaye ko gonaki a Zimbabwe ya haddasa tashe tahen hakula akan harkokin siyasa har m a da jinsin kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG