Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar IS Ta Dauki Alhakin Sabon Hari Afghanistan


Sojoji a Afghanistan

Wani harin kunar wake da aka kai a kan jami'an tsaron Afghanistan a yau litinin ya kashe 'yan leken asiri tare da fararen hula.

Jamia'an kasar Afghanistan sunce wani dan kunar bakin wake a fadar gwamnatin kasar, yau littini ya kashe wasu jamia'an leken asiri biyu, da kuma wasu fararen hulla 4 kana ya jima wasu biyu rauni.

Wannan bomb din dai an tada shi ne a kusa da wani shingen jamian tsaro dake da yawan zirga-zirgar jama'a a babban birnin kasar.

Bisa dukkan alamu dan kunar bakin waken yayi niyyar auna jamia'an tsaro ne , amma kuma sai akayi rashin sa’a abin ya shafi wata motar fararen hula, kamar yadda Najib Danish mai Magana da yawun ministan cikin gida ya bayyana.

Kungiyar IS dai ta dauki alhakin aikata wamnnan danyen aikin.

Wannan harin na yau dai yana zuwa ne sati daya bayan dakungiyar ta IS ta dauki alhakin kai hari a inda kayayyakin horaswa na hukumar tsaro suke a Kabul.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG