Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yarima Harry Na Ingila Yayi Ma Barack Obama Tambayoyi Kan Yanar Gizo


Yarima Harry da Barack Obama
Yarima Harry da Barack Obama

Tsohon Shugaban Amurka Barak Obama yace ya ce yana da muhimmanci mutanen dake amfani da yanar gizo su dagawa mutane kafa don basu damar fahimtar juna.

Tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya fadawa yarima Harry na Burtaniyya hadarin dake tattare da yanar gizo shine “mutane na iya kirkiro nasu tunanin” su kuma nemi bayanan da zasu karfafa ra’ayoyinsu.

Harry yayi hira da Obama a watan Satumban da ya gabata wanda tashar BBC zata yada a yau labara.

Tsohon shugaban na Amurka da ya sauka daga kan mulki a watan Janairun shekarar da ta gabata, bayan da yayi shekaru 8 a kan mulki, ya ce yana da muhimmanci mutanen dake amfani da yanar gizo su dagawa mutane kafa don basu damar fahimtar juna.

“A yanar gizo akan zuzuta komai, kuma idan ka hadu da wadanda aka zuzuta sai ka ga komai ya kasance da wahalar fahimta,” a cewar Obama. Ya cigaba da cewa, “sai a sami maslaha ko fahimtar juna, domin zaka fahimci cewa al’amura basu da sauki kamar yadda ake nunawa a zaurukan hira na Internet.

Tsohon shugaban na Amurka yace “yana kewar aikin shugabancin Amurka, saboda aikin yana da ban sha’awa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG