Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Leken Asirin Amurka Sun Yabawa 'Yan Majalisar Dokokin Kasar


Darektan Hukumar Leken Asirin Amurka-Dan Coats a
Darektan Hukumar Leken Asirin Amurka-Dan Coats a

Jami’an leken asirin Amurka sun yabawa ‘yan majalisar dokokin kasar domin amincewa da shirin sa ido mai sarkakiya, da ‘yan fafatukar kare sirrin jama’a suke kushewa, da cewa, bai kare ‘yaancin talakawa ba.

Majalisar dattijai ta kada kuri’a jiya alhamis da ‘yan majalisa sittin da biyar suka amince, talatin da hudu kuma suka ki amincewa, da zai sabunta dokar harkokin leken asiri na kasashen ketare lamba da dari bakwai da biyu da ake kira FISA na tsawon shekaru shida.

‘Yan majalisar sun kada kuri’ar goyon bayan sabunta shirin makon da ya gabata. Ana kuma kyautata zaton Shugaba Donald Trump zai sa hannu a kai yau jumma’a.

Sashe na dari bakwai da biyu na dokar ya ba cibiyoyin leken asirin Amurka hurumin su saurari da kuma karanta sakonnin da ake aikawa daga kasashen ketare ta hanyoyin sadarwar zamani na dandalin kamfunna irin su Facebook, Google, da kuma Verizon domin tattara bayanai kan ‘yan kasashen ketare da ake sawa ido.

Jami’an leken asirin Amurka sun jima suna bayyana shirin a matsayin mai matukar muhimmanci, suka ce, sun sami bayanai da dama ta wannan hanyar da suka taimaka wajen dakile ayyukan ta’addanci.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG