Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kowace Shekara Ana Sace Dalar Amurka Biliyan 148 Daga Afirka


Taron kolin shugabannin Afirka

Kwatankwacin kashi 25 cikin dari na dukiyar nahiyar Afirka ko dalar Amurka biliyan 148 ne ake sacewa ana boyesu a wasu kasashe tare da wasu bankunan sirri a wurare irinsu Panama

Cin hanci da rashawa yana janye makudan kudi, dala miliyan dubu dari da arba'in da takwas ($148 Billion) ko wace shekara daga Afirka, inji kungiyar hada kan kasashen Afirka AU. Watau kashi 25 cikin dari na dukiyar da al'ummar nahiyar suke samarwa, kamar yadda kungiyar ta AU tayi kiyasi, wadda yake matukar yashe dukiyar da gumin al'ummarta suka samar.

A taron kolin kungiyartarayyar Afirka karo na 31 da aka yi makon jiya a Mauritania,shugabannin kasashen Afirka sun ce suna son su hana sace karin dubban miliyoyin dala ta wajen ganin an soke sirri dake tattare da ajiyar banki da kuma rangwamen haraji a kasashen ketare.

Paul Kagame yayi aiki mai kyau inji Kane. Duk da haka akwai wasu shugabannin kasashen Afirka da suke fakewa da saukin haraji wajen satar dukiya su boye a ketare inji Kane.

Hadakar 'Yan jarida daga kasashen duniya daban daban suna haska fitila kan harkokin banki da ake gudanarwa cikin sirri, da suka wallafa kasidu kan wannan harka da aka lakabawa suna "Panama and Paradise Papers" da turanci.

Binciken da suka gudanar ya bankado kamfanoni da ajiyar bankuna na sirri da manyan 'yan siyasa da 'yan kasuwa daga nahiyar suke amfani da su wajen boye dukiya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG