Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afirka 30 Na Taron Kwana Biyu a Mauritania


Shugaban Nigeria Muhammad Buhari da Shugaban Mauritania Mohammed Ould Abdel Aziz a Nouakchott, babban birnin Mauritanie,
Shugaban Nigeria Muhammad Buhari da Shugaban Mauritania Mohammed Ould Abdel Aziz a Nouakchott, babban birnin Mauritanie,

Cin hanci da rashawa, karancin agaji da matsalar tsaro na cikin abubuwan da shuagabbin kasashen Afirka 30 zasu tattauna akai a taronsu na kwana biyu a Mauritania

Shugabannin Afirka 30 na taron kwanaki biyu a Mauritania, inda suke maida hankali kan yaki da cin hanci da rashawa da kuma yadda za a tunkari matsalolin karancin agaji da tsaro da yankin ke fama da su.

Yayin bude wannan taron koli, mai masaukin baki, shugaban Mauritania, Shugaba Mohammed Ould Abdel Aziz, ya yi gargadi kan yadda ake samun gazawa a fannin tsaro a yankin, a daidai lokacin da aka kashe wasu fararen hula hudu a wani hari da aka kai akan dakarun Faransa da ke sintiri a kasar Mali.

Shugaban ya kuma yi kiran da a dauki kwararan matakai wajen kawar da tsauraran hare-haren da ake samu.

A cewar shugaba Aziz, “nasarar wannan yaki, ta ta’allaka ne akan irin mafitar da za a samar wajen rufe gibin da talauci da sauran matsalolin zamantakewa ke haifarwa a tsakanin matasa, wadanda ke tunzura su su rika daukan tsauraran ra’ayi.”

Shugaban na Mauritania har ila yau, ya yi yi gargadin cewa, muddin nahiyar ba ta magance matsalar cin hanci da rashawa ba, hakan zai hana Afirka ci gaba ta fuskar bunkasar tattalin arziki.

Ana kuma sa ran shugabannin na Afirka za su tattauna kan matakan samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu da kuma shirin sasanta kasashen Ethiopia da Eritrea.

Sauran batutuwan da za su yi dubi akai sun hada da zaben kasar Mali da Kamaru da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da kuma Zimbabwe.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG