A yau Jumma’a ne ‘yan majalisar wakilan kasar Burtaniyya zasu kada kuri’a gameda wani bangaren yarjejeniyar shirin fita daga tarayyar Turai. ‘Yan majalisar zasu kada kuri’a ne akan yarjejeniyar ficewar kawai, abinda masharhanta suka ce zai yi wuya ta yi nasara.
Firayin ministar Burtaniyya Theresa May na kara kokarin shawo kan ‘yan majalisar karo na karshe don su amince da yarjejeniyar fidda Burtaniyya daga tarayyar Turai.
Ballewar kasar daga tarayya Turai dai ya zama wani abu mai wuya fiye da a baya a shekaranjiya Laraba, a lokacin da ‘yan majalisar kasar suka yi watsi da wasu kudurori guda 16 akan bukatar Firayin minista May ta fita daga tarayyar Turai. Mashawarta akan lamarin sun rage yawan kudurorin zuwa 8, da aka kada kuri’a akan su. Cikin kudurorin harda mai neman barin Burtaniyya ta ci gaba da kasancewa cikin yarjejeniyar cinikayya da tarayyar, da kuma wani kudurin wanda ka iya sanyawa a kara kada kuri’ar jin ra’ayin jama’a akan fita daga tarayyar ta EU.
Za ku iya son wannan ma
-
Afrilu 01, 2023
Ranar Talata Trump Zai Mika Kansa Ga Hukuma
-
Maris 29, 2023
Ukraine Ta Kaiwa Rasha Wani Mummunan Hari
-
Maris 29, 2023
Kasar Azerbaijan Ta kaddamar Da Binciken Harin 'Yan Ta'adda
Facebook Forum