Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Daruruwan Mutane Suka Kara Mutuwa a Spain


Yadda aka gudanar da jana'iza kan wasu mutanen da suka mutu sanadiyyar Coronavirus
Yadda aka gudanar da jana'iza kan wasu mutanen da suka mutu sanadiyyar Coronavirus

Kasar Spain ta sanar da karin mace-mace 812 sanadiyyar cutar Coronavirus, yayin da kuma aka tabbatar cewa mutane sama da 6,000 sun kamu da cutar.

Hakan ya sa kasar zama ta uku a jerin kasashe irinsu Amurka da Italiya, wadanda su ka zarce China a yawan masu dauke da cutar.

Hukumomin kasar Spain sun kafa dokar hana yawo makonni biyu da suka gabata, a kokarinsu na kawo karshen yawan yaduwa da cutar ke yi.

Wannan dabarar dai gwamnatoci a fadin duniya na amfani da ita, ciki har da sabbin takunkumi na jiya Litinin a kasar Rasha, na rashin yarda mutane su bar gidajensu sai ko don wasu ayyuka na musamman, da cefanen abinci da magunguna, ko kuma rashin lafiya mai tsanani.

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari shi ma ya sanar da dokar zama a gida a Abuja, babban birnin tarayyar kasar da Lagos mai dinbin jama'a, da kuma Ogun.

Ya ce "ya kamata a kauce wa duk wasu tafiye-tafiye daga wasu bangarori zuwa wasu bangarorin kasar."

Hukumomi a kasar Zimbabwe su ma sun kafa dokar hana zirga-zirga daga jiya Litinin ta tsawon makonni uku, yayin da kuma aka kara tsawaita irin wadannan matakan a Nepal da Slovenia da kuma Argentina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG