Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ci Gaba Da Yi Wa Dimokradiyya Zagon Kasa a Hong Kong


Antony Blinken, Sakataren Harakokin Wajen Amurka
Antony Blinken, Sakataren Harakokin Wajen Amurka

Majalisar dokokin Hong Kong ta zartar da sabuwar doka wacce ta yi wa tsarin zaben Hong Kong garambawul, wanda ya ba wa Beijing babban iko kan Hong Kong.

Za a fadada yawan kujeru a majalisar dokokin Hong Kong zuwa 90, inda 40 daga cikinsu wani babban kwamiti mai goyon bayan Beijing ne zai zabe su. Za a rage yawan 'yan majalisar da masu zaben na Hong Kong suka zaba kai tsaye zuwa 20, daga 35 na baya. Bugu da kari, jami'an tsaron kasar na yanzu za su gudanar da binciken kanyan takarar siyasa don tabbatar da cewa sun kasance "masu kishin kasa," ma'ana masu goyon bayan -Beijing.

Sabuwar majalisar da ake kira "sake fasalin" ta samu karbuwa sosai daga majalisar dokoki wacce kusan babu 'yan majalisun adawa, tun da mafi yawan suka yi murabus a zanga-zangar bara lokacin da aka kori membobinsu hudu saboda rashin cikakkiyar biyayya ga Beijing.

Sabuwar dokar ita ce ta kwana-kwanan nan a cikin jerin matakan da aka kakaba cikin shekaru da dama da suka gabata wadanda ke tauye ‘yancin da aka ba wa mutanen Hong Kong a karkashin yarjejeniyar hadin gwiwar Burtaniyya da China kan mulkin Hong Kong a ƙarƙashin ikon China, wacce ta bada damar bin wata ka’ida ta “ kasa daya, tsarin biyu. ” Tun daga shekarar 2019, an kame dubun-dubatan masu rajin kare demokradiyya da masu zanga-zanga bisa zargin jefa tsaron kasa cikin hadari.

A cikin wata sanarwa, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya nuna rashin jin daɗin yadda gwamnatin China ke ci gaba da rage karfin ikon hukumomin cibiyoyin dimokradiyya na Hong Kong, “da kuma hana mazauna Hong Kong hakkokin da China ita da kanta ta tabbatar musu. Majalisar Dokokin Hong Kong (LegCo) a ranar 27 ga Mayu na sabbin matakan da suka sauya tsarin kafa LegCo da Hukumar Zabe, "in ji shi," yana takura mutane a Hong Kong da shiga harkokin mulkinsu da kuma jin muryoyinsu. ”

Sakatare Blinken ya lura da cewa, sabuwar dokar "ta saba wa amincewar Dokar Asali cewa babbar manufar ita ce zaben dukkan mambobin kungiyar ta LegCo ta hanyar jefa kuri'a."

Sakatare Blinken ya ce "Muna sake kira ga PRC da hukumomin Hong Kong da su ba da damar jin muryoyin dukkan yan Hong Kong." “Muna kuma kira ga wadannan mahukuntan da su saki tare da soke tuhumar da ake yi wa duk mutanen da ake tuhuma a karkashin Dokar Tsaro ta Kasa da sauran dokoki don kawai sun yi zabe ko don bayyana mabanbanta ra’ayoyinsu.

Kasar Amurka ta na tare da kawayenta wajen yin magana game da 'yancin dan adam da' yancin walwala da aka ba wa mutanen Hong Kong ta hanyar Hadin gwiwar Burtaniyya da China kan mulkin Hong Kong a ƙarƙashin ikon China. "

XS
SM
MD
LG