Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Awaren Biafra Na Kara Tilasta Dokar Zaman Gida Kan Shari'ar Nnamdi Kanu


Nnamdi Kanu, Jagoran Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Biafra,
Nnamdi Kanu, Jagoran Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Biafra,

Wasu masu ra'ayin Biafrar na kara tursasa wa al'ummar kudu maso gabashin Najeriya bin dokar zaman gida, tare da bankawa motoci da ababan hawa da ke tafiya wuta, da kuma lalata kayan sayarwa a duk inda suka tayar da shago a bude.

Hakan na faruwa ne yayin da shari'ar madugun kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB Mazi Nnamdi Kanu ke ci gaba da gudana.

wannan lamarin ya sa 'yan kabilar Igbo da dama suka tabka asara sosai sakamakon ayyukan 'yan aware.

A hirar ta da Muryar Amurka, wata ma ce da aka faffasa wa gilashin mota ta koka tana cewa "Mota ta ce wannan suka faffasa gilashinta. Kullum sai mu ce muna neman Biafra. Kawai na fita in sayi abu a Ozara Four Corner da safen nan suka faffasa min mota. Shin da haka ne zamu samo Biafra? Motocin da aka faffasa a Ozara Four Corner yau sun fi hamsin, da shaguna komai sun barnata. Da hakan zamu samo Biafra? 'Yan Igbo ku fa yi tunani game da kanku."

Akan wannan lamarin ne muryar Amurka ta tuntubi wani mazaunin garin Inugu Alhaji Ibrahim Sama'ila, wanda ya bayyana cewa, dokar ta yi kamari sosai akan duk wadanda suka saba wa dokar, ya kara da cewa sun ji cewa an kona wata motar ;yan sanda akan hanyar Port Harcourt, sai dai babu wata majiya ko kuma hukuma da ta tabbatar da haka.

Da Muryar Amurka ta tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Inugu Mista Daniel Ndukwe ya ce, "bani da labari kamar haka a halin yanzu. Idan na samu wannan labarin zan shaida maku daidai abinda na sani."

Kazalika an samu rudani lokacin da wasu 'yan awaren Biafra suka kutsa Majami'ar Katolika ta St. Theresa of Calcutta da ke unguwar Awada a garin Onitsha na jihar Anambra, rike da sanduna da man fetur a safiyar Talata, inda suka tambayi dalilin gudanar da ibada a ranar da aka kebe don zaman gida, ranar da Nnamdi Kanu zai gurfana a gaban kuliya. Bayan sun fita daga cikin Majami'ar, suka tarar da wani matukin Keke NAPEP na yawo, sai suka rufe shi da duka suka bankawa kekensa wuta, kamar yadda wasu manyan jaridun kasar suka ruwaito.

A nashi bayanin, Kwamred Emmanuel Nnadozie Onwubiko wani mai rajin kare hakkin bil'Adama ya ce, idan ana son ganin bayan wannan matsala tilas ne gwamnati ta dauki matakin shawo kan zaman kashe wando da matasa ke yi. Ya kara da cewa, "Akwai bukata gwamnati ta sako kayayyakin more rayuwa. Akwai bukata ta yi aiki kan batun hanyoyi, da wutar lantarki, da kuma wasu muhimman abubuwan da ake bukata. Matasan Igbo da dama sun koyi sana'a, suna da kwarewa, kuma zasu iya kafa nasu kananan masana'antu, idan suka samu tallafi daga gwamnati. Da haka, kowa zai mayar da hankali kan sana'a, ya daina bin wasu masu mumunar akida."

XS
SM
MD
LG