Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahukunta A Nijer Sun Saki Fursinonin Siyasa


Shugaban Nijar, Bazoum Mohamed (Instagram/PNDS Tarayya)

Hukumomin shari’a a jamhuriyar Nijer sun bada sanarwar sallamar akasarin mutanen da suka kama a yayin zanga zangar watsi da sakamakon zaben da aka gudanar a kasar a farkon shekarar 2021 a yayin da a daya bangare ake ci gaba da daukan matakan inganta yanayin rayuwar fursinoni a gidajen yari.

Mutane sama da 400 ne aka bayyana cewa hukumomi sun kama a birnin Yamai da wasu biranen da aka yi fama da tarzomar watsi da sakamakon zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a watan Fabrerun 2021, lamarin da tun a washegarin faruwarsa ‘yan adawa suka ce bita da kullin siyasa ne aka kaddamar akan magoya bayansu.

Bayan shafe shekara fiye guda ana gudanar da bincike hukumomi sun salami galibin wadannan mutane a wannan mako kamar yadda alkali mai tuhuma Chaibou Moussa ya bayyana a taron manema labaran da ya kira.

Koda yake mahukunta na zargin masu zanga zangar ta Fabrerun 2021 da laifin tada zaune tsaye a daya bangare wasu mutanen na daban sun shigar da kara don ganin an biya dukiyoyin da aka bannata a yayin wannan tarzoma.

Yanayin rayuwar fursinoni a wannan lokaci da gidajen yari suka yi cikar kwari wani abu ne da ke haddasa cece kuce a yanzu haka inda wasu ke korafi da matakin hana kai ziyara a wasu wuraren irinsu gidan kason Koutoukale , ba abincin kirki ba kuma matakan kula da kiwon lafiya . Ibrahim Jean Etienne shine magatakardan ofishin ministan shara’a.

Ya ce da jin wannan labari muka aika jami’ai domin gudanar da bincike a kan yanayin da ake tsare da fursinoni wadanda a karshe suka bayar da wasu shawarwari. Saboda haka muka dauki matakin bai wa mutane damar kai ziyara su kuma kai wa mutanensu abinci da magunguna kamar yadda mu ma muka kara inganta tsarin kulawar da ya kamata a bai wa ‘yan kaso.

A farkon makon da muke ciki kungiyar Amnesty international a rahoton da ta fitar ta gargadi hukumomin Nijer akan bukatar mutunta ‘yancin firsinoni a gidajen yarin kasar musamman wanda ke kauyen Koutoukale.

koda yake mahukunta na danganta matakin hana kai ziyara a gidajen yari a matsayin wani bangare na riga kafin cutar corona yayin da a daya gefe ake ganin sakin kofofin gidajen kaso na iya zama wata dama ga yan ta’addan da ke aika aika a yankin Tilabery.

Ga dai rahoton Souley Moumouni Barma daga birnin Yamai:

XS
SM
MD
LG