Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ciki Da Gaskiya: Ana Tuhumar Huzaifa Da Zargin Kashe Mahaifinsa a Kotu, 20 Yuni 2022


Sarfilu Hashiim Gumel
Sarfilu Hashiim Gumel

Sabon shirin zai shiga rukunin gidajen Adisa da ke anguwar APO a Abuja, inda a shekara ta 2018 daidai sallar asuba a ka yi kisan gilla ga Alhaji Hussaini Usman da bincike ke nuna an shake shi ne da igiya bayan rufe kan sa da bakar hula.

‘Yan sanda sun garzaya gidan don aikin gano wadanda su ka yi kisan, daga karshe sun cafke dan marigayin mai suna Huzaifa da a ke zargi shi da kashe mahaifin sa lahira. Yanzu haka a na gudanar da shari’a don kotu ta yanke hukunci kan wadanda a ka samu da laifi.

Saurari shirin kashi na farko:

Ciki Da Gaskiya: Ana Tuhumar Huzaifa Da Zargin Kashe Mahaifinsa a Kotu - 12'11"
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:11 0:00

XS
SM
MD
LG