Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bazoum Ya Fara Rangadi a Jihar Diffa Don Samar Da Zaman Lafiya a Jihar


Mohamed Bazoum yayin wani rangadi
Mohamed Bazoum yayin wani rangadi

Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya fara wani rangadi a jihar Diffa, domin jin halin  da ake ciki game da kokarin da gwamnatinsa  take yi na ganin zaman lafiya ya dawo a jihar, wacce ke fama da hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram da kuma na  mayakan ISWAP tun cikin shekarar 2015.

Wannan rangadin shine na biyu da shugaban kasar ta Nijar ya kai a jihar Diffa tun bayan hawansa kan karagar muliki.

A rangadin da ya gudanar shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya fara ne da kai ziyara barakin sojoji na biyar dake cikin jihar ta Diffa, inda ya jinjinawa dakarun hadin gwiwa na kasashen yankin tafkin Chadi da suka hada da Kamaru da Nijar da Najeriya da kuma Chadi.

Dakarun hadin gwiwar dai na ci gaba da samun nasara kan kungiyoyin 'yan ta'addan, wanda tun daga ranar 28 ga watan Maris zuwa 4 ga watan Yunin wannan shekarar sun hallaka 'yan ta'adda kimanin 800, tare da kone dukkan kayayyakinsu da suka hada da motoci da babura da sauransu.

Mohamed Bazoum yayin wani rangadi
Mohamed Bazoum yayin wani rangadi

Abu daya da yafi daukar hankalin shugaban Bazoum shine batun mayar da 'yan gudun hijira garuruwansu na asali. wanda a baya ya taba sake tsugunnar da 'yan gudun hijira a gidajensu da aka talasta raba su da su.

A wannan karon kuma, ana sa ran shugaban kasar ta Nijar ya mayar da ‘yan gudun hijira na garruruwan Diffa 44 a garuruwansu na asali domin su samu damar gudanar da aikin noma.

XS
SM
MD
LG