Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CIKI DA GASKIYA: Mutum 4 Sun Bace a Hannun Jami’an Tsaro a Jihar Taraba


Sarfilu Hashiim Gumel
Sarfilu Hashiim Gumel

Sabon shirin zai kai mu jihar Taraba kuma yankin karamar hukumar Bali a garin Gazabu, inda ‘yan uwan wasu matasa 3 da dattijo mahaifin daya daga matasan, su ka baiyana cewa tun farkon shekarar nan ta 2022, ‘yan uwan na su su ka bata bat ko sama ko kasa, biyo bayan gaiyatar da ‘yan sanda su ka yi mu su a garin na Gazabu da sunan bincike.

Matasan sun hada da Musa Umar wanda asalin sa dan yankin Shani ne da ke kudancin Borno, sai abokan sa Abbas Muhammad da Adamu Ayuba da kuma mahaifin Adamu wato Malam Ayuba.

Dan uwan matasan mai suna Salman Gase ya baiyana ma na cewa tun farko dai an gaiyaci Adamu ne, inda ganin bai dawo ba, mahaifin sa ya nemi jin bahasi da hakan ya sa, su hudu duka su ka fada hannun hukuma ko a ce daga karshe hannun sojoji.

Saurari kashi na farko:

CIKI DA GASKIYA: Mutum 4 Sun Bace a Hannun Jami’an Tsaro a Jihar Taraba - 11'25"
please wait

No media source currently available

0:00 0:11:25 0:00

XS
SM
MD
LG