Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Mutane 3,000 Suka Rasa Matsugunnansu Sakamakon Wani Sabon Fada A Kan Iyakar Kamaru Da Najeriya


Rundunar Tafkin Chadi MNJTF Ta Ceto Wasu Mata 43 Da Yara 30 Da Suka Tsere Wa ‘Yan Boko Haram/ISWAP
Rundunar Tafkin Chadi MNJTF Ta Ceto Wasu Mata 43 Da Yara 30 Da Suka Tsere Wa ‘Yan Boko Haram/ISWAP

Rundunar da ke yaki da mayakan Boko Haram a kan iyakar Najeriya da Kamaru ta ce akalla mutane 3,000 ne suka rasa matsugunansu a wani sabon fadan mayakan Boko Haram da ya barke kwanan nan.

Mutanen da suka rasa matsugunansu a sansanin ‘yan gudun hijira na Minawao da ke kan iyakar Kamaru da Najeriya, sun ce adadin mutanen da ke neman agajin jinkai a sansanin na karuwa a kowace rana.

A lokacin da ya yi magana da Muryar Amurka, Isaac Luka, shugaban ‘yan gudun hijira na Najeriya a Minawao, ya ce kwararowar ‘yan gudun hijira da ake gani yanzu saboda yunwa da tashin hankalin bindiga na kara tsanta yanayin rayuwa a sansanin.

“Akwai ‘yan Najeriya da suka fito daga garuruwan da ke kusa da iyakar. Ana ba su filiye don su fara noman abinci, amma yanayin damina ya shafi amfanin gona a kakar bana, kuma yawan kai hare-haren ‘yan bindiga a yankunan bakin iyakar sun sa kan dole jama’ar suka koma sansanin ‘yan gudun hijira. Suna da ‘yan uwa a sansanin. Dan abin da suke da shi suna rabawa a tsakaninsu. Wasu na sana’ar saida itace don samun abinda zasu kula da 'ya'yansu," a cewar Luka.

Sojojin Najeriya Na Fatattakar Yan Boko Haram
Sojojin Najeriya Na Fatattakar Yan Boko Haram

A watan Yunin shekarar 2014 ne Luka ya tsere daga jihar Bornon Najeriya bayan da 'yan ta'addan Boko Haram suka kashe sama da mutane 20 a kauyensu, ciki har da ‘yan uwansa.

Toudje Voumou, shi ne babban jami'in gwamnati a gundumar Mayo-Moskota, ya ce rundunar hadin gwiwa da ake kira MNJTF a takaice, ta kara yawan dakarunta a kan iyakar kasar. Rundunar dai na da dakaru daga Najeriya, Nijar, Kamaru da kuma Chadi.

Dakarun hadin guiwa a yankin Chadi
Dakarun hadin guiwa a yankin Chadi

Voumou ya ce kusan makonni biyu kenan ana gwabza kazamin fada tsakanin sojojin gwamnatin Kamaru da mayakan Boko Haram a bangaren kan iyakar na Kamaru da Najeriya. Voumou ya kuma ce an kafa sansanonin soja da dama domin tunkarar mayakan Boko Haram da ke fakewa a yankin suna muzgunawa farar hula a kauyukan da ke kan iyakar.

Rundunar dakarun MNJTF ta sanar a watan Fabrairu cewa za ta sadaukar da watan Maris domin murkushe sauran ragowar mayakan Boko Haram a yankin kan iyakar.

XS
SM
MD
LG