Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Daukar Darasi A Kura-kuran Baya Ya Kai Ghana Ga Tabarbarewar Tattalin Arziki


Tabarbarewar Tattalin Arziki Da Tsadar Rayuwa Sun Fi Tasiri A Shekarar 2022 A Ghana
Tabarbarewar Tattalin Arziki Da Tsadar Rayuwa Sun Fi Tasiri A Shekarar 2022 A Ghana

Cibiyar kula da harkokin tattalin arziki ta bayyana damuwarta game da maimaita kura-kurai da gwamnatoci suka yi a baya wanda ya sanya tattalin arzikin Ghana ya tabarbare tsawon shekaru.

A cewar cibiyar nazarin tattalin arzikin, rashin da'a wajen tafiyar da harkokin kudi na kasar ya haifar da gibin kasafin kudi da kuma hauhawar farashin kayayyaki da kuma rashin tabbas ga kudin kasar, lamarin da ya tilastawa 'yan Ghana da 'yan kasuwa da ba su ji ba ba su gani ba suna shan wahalar matsalar.

A cikin wata takarda mai taken "Tabbatar da da’a ga tsarin da kudi da daidaita tsarin tattalin arziki don ci gaba mai dorewa a Ghana: Hanyar da Tsarin Mulki ta tanada", Jagoran Bincike, Dokta John Kwakye ya ce Ghana na da dogon tarihi na rashin da'a na kasafin kudi kuma wannan ya bayyana a cikin gibin kasafin kudin da yake zama kusan mafi girma fiye da takwarorinta na Afirka.

“Gibin da muke samu yana karuwa a shekarun zabe idan muka kara yawan kashe kudaden da suka shafi sha’anin zabe. Sa'an nan kuma mu ciyo bashi don cike gibin da kuma haifar kana bashin jama'a ya karu zuwa matakin da ba za a iya dorewa ba. Mun kasance a cikin wannan yanayin sau da yawa. Bashinmu ya fara kaiwa matsayi na rikicin ne kusa shekarar 2004, lokacin da ya kai sama da kashi 100 bisa 100 na baki dayan abin da kasa ke samarwa ko kuma GDP a turance.

Ya ce “Dole ne mu nemi taimako a karkashin shirin tallafawa kasashe masu tsananin talauci na HIPC, wanda ya sa yawan basussuka zuwa GDP ya ragu har ya kai wani matsayi mai dorewa na kashi 26 cikin 100 a shekarar 2006. Bayan haka, mun koma ga al’adunmu na rashin da’a na kasafin kudi, wanda ya sa har yanzu bashin ya sake hauhawa. Kuma a yau, awon bashi-zuwa-GDP ya koma matakin da ba zai iya dorewa ba na sama da 100 bisa 100,” in ji shi.

A cewar shafin yanar gizo na Myjoyonline, Dr. Kwakye ya sake nuna damuwarsa kan yadda gwamnati mai ci da wadda ta shude ba su yi koyi da kura-kuran da suka yi a baya ba bayan kusan shekaru 20 na shiga shirin HIPC.

“Mun dawo inda muke kusan shekaru ashirin da suka wuce! Da alama ba ma daukar darasi daga kurakuranmu! Muna jin manyan jam’iyyun biyu suna zargin juna kan wane ne ya kara yawan bashin. Ba wai wane ne ya fi rage bashin ba, tun da yake hanya daya ce suke bi wurin kara yawan bashin ya kai sama!”

Ya kara da cewa dole ne kasar nan ta yi duk mai yiwuwa don kiyayewa ko tabbatar da da’a a tsarin kasafin kudi a karkashin kundin tsarin mulki, in ba haka ba zata cigaba da fuskantar tabarbarewar tattalin arziki.

XS
SM
MD
LG