Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shari'ar Trump: Stormy Daniels Ta Ba Da Ba'asi


Donald Trump
Donald Trump

A ci gaba da shari'ar tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, wadda ake yi a New York, tauraruwar fina finan batsa, Stormy Daniels, ta yi bayani mai cike da batsa jiya a kotun.

Jiya Talata, jarumar fina-finan batsa, Stormy Daniels, ta yi tozali da tsohon shugaban kasar, Amurka Donald Trump a kotu, inda ta bayyana wa masu taimaka wa alkali yanke hukunci a shari’ar da ake masa a birnin New York cewa ta kwana da shi amma ba don ta na so ba a shekarar 2016, sannan daga baya aka biya ta dala dubu $130,000 domin tayi shiru game da lamarin gabanin tsayawa takara da Trump ya yi cikin nasara a zaben shugaban kasa na 2016.

Stormy Daniels ta ba da shaida ta tsawon sa’o’i game da yadda ta hadu da Trump a gasar shahararru ta kwallon golf ta Lake Tahoe a Nevada, yadda ya gayyace ta zuwa cin abincin dare a dakin otal dinsa, yadda ya nuna ma ta "rashin mutunci da ji da kai," da yadda suka tattauna yiwuwar saka ta a shirinsa na “Celebrity Apprentice,” na raha, sannan suka kwanta a gado na takaitaccen lokacin suka yi mu’amala ta jima’i, abin da shi kuma Trump ya musanta faruwarsa.

Lauyan da ke kare Trump, Todd Blanche ya nemi a ayyana ba'asinta marar cancanta bayan da a wasu lokuta ta yi ta furta kalaman batsa a bayanan da ta yi. Amma alkalin kotun kolin New York, Juan Merchan, yayin da ya ce ya so a ce ba ta fadi wasu kalamanta ba, ya ki amincewa da bukatar (lauyan Trump din).

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG