Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Zanga-Zanga: Tinubu Na Ganawar Gaggawa Da Sarakunan Gargajiya Da Babban Sufeton ‘Yan Sanda


Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu

Wannan taro na gudana ne a fadar gwamnatin tarayyar Najeriya dake Abuja.

A yayin da shirin gudanar da zanga-zangar ‘EndBadGovernance” da za’a yi a watan Agusta ke kara gusowa, a yau Alhamis Shugaban Kasa Bola Tinubu ya shiga wata ganawar gaggawa ta sirri da manyan sarakunan gargajiya da jami’an tsaro da ma gwamnonin jam’iyyarsa ta APC.

Wannan taro na gudana ne a fadar gwamnatin tarayyar Najeriya dake Abuja.

Gwamnonin jam’iyyar APC na halartar taron karkashin jagorancin shugabansu kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma.

An hangi wasu sarakunan gargajiya daga sassan kasar daban-daban a ganawar da Shugaba Tinubu wadanda suka hada da; Ooni na Ife, Oba Enitan Ogunwusi da Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar Iii da sauransu.

Ganawar ta samu halarcin mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu da Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun har ma da ministoci da manyan jami’an majalisar zartarwar shugaban kasar.

Dandalin Mu Tattauna

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG