Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Tarayyar Turai Ta Janye Jakadanta Daga Nijar


Shugaban majalissar sojojin juyin mulkin jamhuriyar Nijer Janar Abdourahamane Tchinai
Shugaban majalissar sojojin juyin mulkin jamhuriyar Nijer Janar Abdourahamane Tchinai

EU ta janye jakadan na ta ne domin ta ji ta bakinsa bayan da gwamnatin Nijar ta zarge shi da saba ka'ida da saka son rai wajen kasafta wani tallafin jin kai na Euro milion 1.3 da kungiyar ta bayar domin agaza wa 'yan Nijar da ambaliyar ruwa ta shafa.

Wannan na zuwa ne bayan da ma'aikatar harakokin wajen Nijar ta zargi jakadan Tarayyar Turan da raba kimanin euro miliyan 1.3 ga kungiyoyi masu zaman kansu a kasar ba tare da sanar da hukumomi ba.

Kungiyar agaji ta kasa da kasa ICRC da kungiyar kula da 'yan gudun hijra Danish refugee council DRC da kuma Cooperazione internationale COOPI sune kungiyiyon da EU ta bai wa wadanan kudade abinda hukumomin Nijar suka ce an yi shi cikin yanayin mai hazo, hasalima jakadan kungiyar da kansa ne ya karkasa wannan tallafi a tsakanin jihohi duk kuwa da cewa a ka’ida a kan yi irin wannan aiki ne da hadin guiwar gwamnati.

Da yake bayyana ra’ayinsa kan wannan al’amari shugaban gamayyar kungiyoyin Reseau Esperance Bachar Mahaman ya ce, Tarayyar Turai ba ta yi la’akari da sabuwar tafiyar gwamnatin Nijar ba yayin bayar da wannan tallafi.

Kungiyar EU ta bayyana takaicinta akan abubuwan da ta Kira zarge zarge marassa tushe sannan ta kara da cewa bai dace a siyasantar da aiyukan Jin Kai ba.

Kungiyar a sanarwar da ta fitar tace a kullum ta cikin shirin baiwa al’ummar Nijar taimako. kuma tace tana damka wa rassan kungiyoyin Majalisar dinkin duniya da sauran kungiyoyin kasa da kasa domin su tafiyar da tallafin ba tare da katsalandan ba.

Tuni kungiyar ta janye jakadanta daga Nijar domin yin abinda ta kira tantaunawa da shi. Matakin da wani dan Nijar Tchanga Tchalimbo ya ce shine mafi a’ala.

Ma'aikatar harakokin wajen Nijar tace ta kudiri aniyar gudanar da bincike kan wannan al'amari, ta Kuma bukaci kungiyar Tarayyar turai ta gudanar da bincike a nata bangaren domin gano gaskiyar lamari dangane da yadda aka kasafta kudaden tallafi.

Wannan cece kuce na wakana a Wani lokacin da gwamnatin mulkin sojan Nijar ta tsaurara matakan sa ido akan aiyukan Kungiyoyi masu Zaman kansu. A tsakiyar Watan nan na Nuwamba ma'aikatar cikin gida ta dakatar da aiyukan wasu Kungiyoyi cikin gida da na kasa da kasa cikin su har da ACTED ta kasar Faransa duk da yake ba a bayyana dalilan daukan matakin ba.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Kungiyar Tarayyar Turai Ta Janye Jakadanta Daga Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG