An bada rahoton cewar wadanda al’amarin ya rutsa dasu leburori ne daga jihohin Filato da Kaduna dake aiki a gonakin.
Wani ganau ya bada labarin cewar harin ya faru ne da misalin karfe 3 na rana a Talatar da ta gabata, inda ya kara da cewa makiyayan na lalata musu amfani gona tare da kawo cikas a rayuwar al’ummar kauyen.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, CSP Fumnmlayo Odunlami ta tabbatar da afkuwar lamarin.
Sai dai, ta kasa samar da hakikanin alkaluman wadanda suka mutun, inda tace har yanzu ‘yan sanda na gudanar da bincike a kan lamarin.
Daya daga cikin leburorin da ya tsallake rijiya da baya a harin, ya bayyana cewa kwatsam sai makiyayan suka bullo tare da fara harbin kan mai uwa da wabin, da ya hallaka mutane 5.
Dandalin Mu Tattauna