Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Bincike A Nijeriya Sun Ce har yanzu Ba Su Gano Na'urar Tattara Bayanai Na Jirgin Da Ya Fadi Ba


Masu bincike a Nijeriya sun ce har yanzu ba su gano na'urorin tattara bayanan jirgi a wurin da jirgin kamfanin Bellview ya yi hatsari ya kashe mutane 117 a watan da ya shige ba.

Masu bincike na Nijeriya da wasu daga Amurka suna gudanar da wannan bincike na faduwar jirgin saman kamfanin Bellview kirar Boeing 737, wanda a ranar 22 ga watan Oktoba ya fadi a arewa da birnin Lagos.

Masu binciken su na ci gaba da nazarin guntattakin garewani na jirgin ko zasu ga wani abinda zai kara bayar da haske kan musabbabin wannan hatsari.

Wannan jirgin saman fasinja ya bace daga na'urar hango jirage jim kadan a bayan tashinsa daga Lagos a kan hanyar zuwa Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya.

XS
SM
MD
LG