Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar dattijan Nijeriya Ta Yi Fatali Da Kudurin Tazarce


Majalisar dattijan Nijeriya ta yi fatali da shitrin yin gyara ga tsarin mulki domin kyale shugaba Olusegun Obasanjo yayi Tazarce.

’Yan majalisar sun yi watsi da matakin a lokacin da aka jefa kuri’a ta murya yau talata a zauren majalisar, matakin da ya sanya sanatoci masu yin adawa da tazarce suka barke da sowa da rawar murna.

Shugaban majalisar dattijai, Ken Nnamani, ya ce wannan kuri’a ta nuna cewa majalisar dattijai dai a fili tana son kawo karshen duk wata muhawara a kan wannan kuduri na yin gyara ga tsarin mulki.

Ana bukatar kashi biyu bisa uku na kuri’un ’yan majalisu biyu na dokokin tarayya kafin a iya yin gyara ga tsarin mulkin wanda a yanzu ya takaita wa’adin shugaba zuwa ga biyu kawai a kan mulki.

Masu yin adawa da shirin gyaran tsarin mulkin sun zargi magoya bayan shugaba Olusegun Obasanjo da laifin kokarin ba su cin hanci domin su amince da tazarce. Jami’an gwamnati sun musanta wannan zargi.

Mr. Obasanjo, wanda aka fara zaba a 1999, bai fito a bainar jama’a ya ayyana cewar zai sake tsayawa a wa’adi na uku ba.

XS
SM
MD
LG