Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Atiku Abubakar Ya Ce Matakin Da Majalisar Dattijai Ta Dauka Na Yin Fatali Da Shirin Tazarce Abin Tarihi Ne


Mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya taya majalisar dattijan kasar murnar shawarar da ta dauka ta yin fatali da kudurin gyara tsarin mulkin kasar domin kyale shugaba Olusegun Obasanjo yayi Tazarce.

A cikin wata sanarwar da ya bayar dazu, mataimakin shugaban na Nijeriya ya ce wannan matakin da majalisar dattijai ta dauka ya karfafa imanin ’yan Nijeriya cewar dimokuradiyya zata iya samun wurin zama da gindinta a kasar.

Alhaji Atiku Abubakar ya ce ta hanyar kasa kunne ga muradu da ra’ayoyin mafi yawan al’ummar Nijeriya, majalisar dattijan ta nuna cewa zata iya kare dimokuradiyya duk da irin kokarin bayar da cin hanci, ko barazana ko cin mutunci ko musguna ma ’ya’yanta da aka so yi.

Musamman mataimakin shugaban na Nijeriya ya yabawa tsoffin shugabannin kasar da gwamnonin da suka cije da kafofin labarai a saboda turjewar da suka yi domin ganin an tabbatar da adalci.

A yau talata ne dai ’yan majalisar dattijan Nijeriya suka yi watsi da kudurin tazarce a lokacin da aka jefa kuri’a ta murya a zauren majalisar, matakin da ya sanya sanatoci masu yin adawa da tazarce suka barke da sowa da rawar murna.

Shugaban majalisar dattijai, Ken Nnamani, ya ce wannan kuri’a ta nuna cewa majalisar dattijai dai a fili tana son kawo karshen duk wata muhawara a kan wannan kuduri na yin gyara ga tsarin mulki.

Masu yin adawa da shirin gyaran tsarin mulkin sun zargi magoya bayan shugaba Olusegun Obasanjo da laifin kokarin ba su cin hanci domin su amince da tazarce. Jami’an gwamnati sun musanta wannan zargi.

Mr. Obasanjo, wanda aka fara zaba a 1999, bai fito a bainar jama’a ya ayyana cewar zai sake tsayawa a wa’adi na uku ba.

XS
SM
MD
LG