Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Sin Ta Dakatar Da Dukkan Ayyukan Tonon Karfen Uranium A Arewacin Jamhuriyar Nijar


Wani kamfanin kasar Sin ya rufe ayyukan tonon karfen Uranium da yake gudanarwa a arewacin Jamhuriyar Nijar a bayan barazanar da ya samu daga wata kungiyar ’yan tawaye ta Abzinawa.

Jami’an soja da majiyoyi na kusa da kamfanin sun ce Kamfanin Ayyukan Nukiliya na kasar Sin ya dakatar da ayyukansa a bayan da ya samu wannan barazana daga Kungiyar Tabbatar da Adalci ta Nijar.

Majiyoyin suka ce an kwashe dukkan ma’aikatan kamfanin da kayayyakin aikinsu zuwa garin Ingall, mai tazarar kilomita kimanin 100 daga Yamai, babban birnin kasar.

Kungiyar ’yan tawayen ta sace wani jami’in wannan kamfani kwanaki hudun da suka shige, amma kuma a yau talata ta yi alkawarin cewa zata sake shi ta mika shi ga kungiyar agaji ta Red Cross.

Nijar tana daya daga cikin kasashen duniya da suka fi samar da karfen Uranium.

Kungiyar ’yan tawayen dake kiran kanta Kungiyar Tabbatar da Adalci a Nijar, kungiya ce ta ’yan kabilar Abzinawa da wasu kabilun. A cikin ’yan watannin nan, kungiyar ta kai hare-hare a kan cibiyoyin gwamnati da na ’yan kasashen waje a yankin arewacin kasar.

XS
SM
MD
LG