Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Masu Bincike Sun Gano Allurar Rigakafin Zazzabin Cizon Sauro Mai Kaifi.


Masu bincike sun bayyana cin karo da allurar rigakafi mafi alfanu da aka taba gani, ta kare jarirai da yara kanana daga kamuwa da zazzabin cizon sauro, ko maleriya.

A wani rahoton da aka wallafa cikin wannan makon a mujallar kiwon lafiya ta “The New England Journal of Medicine”, masu binciken sun bayyana sakamakon wasu gwaje-gwaje guda biyu da aka gudanar a kasashen Kenya da Tanzaniya, na wannan allurar rigakafin zazzabin cizon sauro mai suna “RTS,S/AS”.

Masu binciken sun gano cewa wannan allurar rigakafi, wadda ita ce ta fi kaifi ya zuwa yanzu daga cikin wadanda aka taba gwadawa, ta hana cutar kama fiye da rabin jarirai da yaran da aka yi gwajinta kansu. Cutar maleriya tana kashe mutane miliyan daya kowace shekara, akasarinsu yara kanana.

Christian Loucq shi ne darektan wata kungiya mai zaman kanta dake samar da kudade don ayyukan binciken rigakafin zazzabin cizon sauro da ake kira “PATH Malaria Vaccine Initiative”. Loucq ya ce koda yake allurar ba wai tana aiki dari bisa dari ba ne, samunta mataki ne da ya dace, yana mai cewa, “...sakamakon gwaje-gwajen da aka bayyana...ya nuna cewa mun dauki muhimmin matakin da ya matsa da mu zuwa ga ranar da cutar maleriya zata shiga sahun cututtuka irinsu agana da shan inna wadanda kodai an kawar da su daga doron kasa, ko kuma ana rigakafinsu sosai.”

A gwajin da aka yi a kasar Tanzaniya, masu bincike sun ba da wannan maganin rigakafi ga jarirai dari uku da arba’in. Suka ce a cikin watanni shida da aka yi ana wannan gwajin, kashi sittin da biyar daga cikin dari na jariran ba su kamu da cutar maleriya ba.

A kasar Kenya, inda aka yi gwajin kan yara masu watanni biyar zuwa watanni goma sha bakwai da haihuwa, wannan maganin rigakafi mai suna “RTS,S/AS” ya kare kashi hamsin da uku daga cikinsu a watanni takwas da aka yi ana wannan gwajin.

Ripley Ballou, jami’i ne a Gidauniyar Bill da Melinda Gates, wadda take kokarin inganta kiwon lafiya da raya kasa da bunkasa ilmi a duniya. Ballou ya ce, “Gidauniyar (ta Bill da Melinda Gates) tana dokin wannan aiki ainun a saboda na ceton rayuka ne. Kuma ya kamata mu fahimci cewa rayukan na jarirai da kananan yara ne wadanda suka fi fuskantar hatsarin mutuwa daga cutar maleriya. Wannan allurar rigakafi ta fi yin kaifi a daidai lokacin da wadannan jarirai da yara suka fi fuskantar kasada ta mutuwa daga cutar maleriya.”

A yanzu dai, masana masu binciken su na zaben jarirai da yara kanana su dubu 16 domin fara gwaje-gwajen karshe na wannan sabuwar allurar rigakafin zazzabin cizon sauro a shekara mai zuwa. Idan har komai ya tafi daidai, ana sa ran zasu nemi iznin hukuma domin fara yin amfani da allurar rigakafin a shekarar 2011.

(Wakiliyar Muryar Amurka, Jessica Berman, ta taimaka wajen hada wannan rahoton)

XS
SM
MD
LG