Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Tsohon Maganin Maleriya Da Aka So Daina Amfani Da Shi Ya Sake Samun Farin Jini


Wani Tsohon Maganin Maleriya Da Aka So Daina Amfani Da Shi Ya Sake Samun Farin Jini

Wani sabon nazari ya nuna cewa wannan magani mai suna Sulfadoxine-Pyrimethamine zai iya rage kamuwa da cutar maleriya da kashi 30 cikin 100 a tsakanin jarirai.

Wasu sabbin nmazarce-nazarce da aka gudanar, sun nuna cewa wani magani marasa tsada wanda yanzu haka ake amfani da shi wajen jinya ko kuma rigakafin cutar maleriya ko zazzabin cizon sauro, Sulfadoxine-Pyrimethamine, ko kuma SP a takaice, zai iya rage yawan jariran dake kamuwa da cutar maleriya da kashi 30 cikin 100.

Amma kuma jami'ai na kasashe masu tasowa sun ki yarda su bayar da shawarar kara yin amfani da wannan magani a saboda fargabar cewa kara yin amfani da shi zai gaggauta jurewar da kwayar cutar dake haddasa Maleriya take yi da wannan magani, abinda zai sa ya zamo ba ya da kaifi ko amfani nan gaba.

Amma kuma wasu sabbin kasidu biyu na bincike da aka gudanar a tsakanin jama'a da kuma a dakin binciken kimiyya kan wannan magani mai suna sulfadoxine-pyrimethamine, sun nuna cewa yana iya zamowa magani mai amfani da kuma kaifi wajen hana kamuwa da cutar maleriya.

Yankunan da cutar maleriya ta fi yin barna a duniya aka shafe da launin ja a wannan taswira ta duniya
Yankunan da cutar maleriya ta fi yin barna a duniya aka shafe da launin ja a wannan taswira ta duniya

Maleriya tana kama miliyoyin mutane a fadin duniya, tana kuma kashe mutane kimanin dubu 900 a kowace shekara, musamman ma yara kanana a kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara.

Duk da binciken da aka shafe shekaru fiye da hamsin ana gudanarwa, har yanzu ba a samu allurar rigakafin cutar ta maleriya da aka amince da ita ba, kuma kwayar cutar dake hassa zazzabin na cizon sauro ta rikide ta zamo mai iya jurewa magunguna da dama da ake amfani da su wajen yakarta. Koda yake har yanzu ba a fahimci yadda kwayar cutar take iya jure ma magungunan baki daya ba, masu bincike sun nuna cewa wannan juriya tana da alaka da yadda kwayar cutar take iya sauya fasalin kwayoyin halittarta ta yadda yawan irin wadannan magunguna dake shiga jikinta suna zamowa guba yake raguwa sosai.

Masu bincike kan cutar Maleriya sun jima su na tsammanin cewa yawaita amfani da maganin sulfadoxine-pyrimethamine zai kara yaduwar cutar maleriya da kuma kwayoyi masu iya jurewa maganin a saboda yin amfani da maganin wajen warkar da wannan cuta yana haddasa karuwar masu fama da cutar. Amma kuma wani mai bincike na Cibiyar Magunguna ta Howard Hughes dake Jami'ar Bamako a kasar Mali, Abdoulaye Djimde, yace binciken ad suka gudanar ya kalubalanci wannan hasashe.

Jariri mai fama da cutar Maleriya a Dakar a kasar Senegal
Jariri mai fama da cutar Maleriya a Dakar a kasar Senegal

Abdoulaye Djimde, yace, "Bincikenmu na baya-bayan nan ya kalubalanci wannan hasashe ko tsammani, domin babu wata kwakkwarar hujja da ta goyi bayan wancan tunanin." Djimde zai gabatar da wannan sabon bincike nasa yau laraba, 18 ga watan Agusta, 2010 a Taron Duniya kan Kwayoyin Cuta masu Yaduwa da za a yi a birnin Melbourne a kasar Australiya.

Ganin cewa har yanzu akwai sauran shekaru masu yawa kafina kai ga samun allurar rigakafin cutar maleriya, ma'aikatan kiwon lafiya a kasashe masu tasowa sun dogara ne a kan jerin magungunan da aka amince da su wajen warkarwa ko kuma rigakafin cutar maleriya. Sai dai kuma yadda kwayar cutar ta fara jure ma wasu daga cikin magungunan ta haddasa matsala babba ga ma'aikatan kiwon lafiyar na kasashe masu tasowa a saboda a yanzu ba zasu iya yin amfani da wasu magungunan masu arha wajen warkar da cutar ba.

Djimde da abokan aikinsa a kasar Mali sun shafe shekaru goma da suka shige su na nazarin yadda kwayar cutar take jurewa magunguna. Ya fara aiki kan maganin sulfadoxine-pyrimethamine a shekarar 2000, a lokacin da kwayar cutar maleriya ta fara gagarar maganin da aka fi yin amfani da shi a lokacin, watau Chloroquine.

XS
SM
MD
LG