Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministocin Nijeriya Su Na Kan Hanyar Zuwa Ganin Umaru Musa 'Yar'aduwa


Wata tawagar ministocin Nijeriya tana kan hanyar zuwa Sa'udiyya, inmda ta ke fatar ziyartar shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa mai fama da rashin lafiya.

Wannan tawagar mutane 6 a karkashin jagorancin ministan harkokin lafiya, Babatunde Osotimehin, tana da niyyar duba matsayin lafiyar shugaban tare da bayar da rahoto ga majalisar ministocin kasar idan ta koma.

A can baya, an hana tawagogi har uku ganin shugaban tun lokacin da aka kai shi jinya a kasar Sa'udiyya a ranar 23 ga watan Nuwamba.

Kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, ya ambaci jakadan Nijeriya a Sa'udiyya, Abdullahi Aminchi, yana fadin cewa likitocin shugaban ne, ba wai hukumomin Sa'udiyya ba, suke hana mutane ganinsa.

Sau daya tak aka ji ta bakin shugaba 'Yar'aduwa cikin wata gajeruwar hira ta rediyo, tun lokacin da aka kwantar da shi a asibitin watanni uku da suka shige.

Kwanakin baya majalisar dokoki ta nada mataimakin shugaba Goodluck Jonathan a matsayin shugaban riko, amma wasu 'yan majalisar dokoki da lauyoyi su na bayyana ra'ayin cewa wannan matakin ya saba da tsarin mulkin Nijeriya.

XS
SM
MD
LG