Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Nijeriya Sun Damu Da Ko Wanene Ke Jagorancin Kasar


‘Yan Nijeriya su na bayyana damuwa kan gwagwarmayar shugabanci a kasar, kwana guda a bayan da shugaba Umaru Musa ‘Yar’aduwa mai fama da laulayi ya koma kasar daga zaman watanni uku a wani asibitin kasar Sa’udiyya.

A yau alhamis, jaridu da masu fashin baki sun yi ta bayyana ayoyin tambaya kan ko wanene ke jagorancin kasar: shugaba ‘Yar’aduwa ne, ko matarsa Hajiya Turai ko kuma mataimakin shugaba Goodluck Jonathan?

Jiya laraba kakakin shugaban, Olusegun Adeniyi, yace mataimakin shugaba Jonathan zai ci gaba da jagorancin kasar a yayin da shugaban yake ci gaba da murmurewa. Mr. Jonathan ya bada sanarwa jiya laraba yana fadin cewa a lokaci irin wannan, tilas dukkan ‘yan Nijeriya su sanya muradun kasa a sama da duk wani muradin radin kai.

XS
SM
MD
LG