Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ce Ranar Badar A Majalisar Wakilan Amurka Kan Dokar Grambawul Ga Tsarin Inshoran Kiwon Lafiya A Amurka


Yau Ce Ranar Badar A Majalisar Wakilan Amurka Kan Dokar Grambawul Ga Tsarin Inshoran Kiwon Lafiya A Amurka

<!-- IMAGE -->

Shugaban Amurka Barack Obama ya gabatar jawabi domin karfafawa ‘yan majalisar wakilan Amurka na Jami’iyyar democrat guiwa,yana mai cewa yanzu lokaci ya yi na amincewa da shirn garambawul ga inshoran kiwon lafiya,kuma yana ji zasu yi hakan lahadin nan.

Mr. Obama ya yi magana ga taron wakilai ‘yan jami’iyyarsa dake majalisar a harabar majalisar.Shugaban Amurkan ya gayawa wakilai yana sane da irin matsin lamba da dokar data janyo cece kuce ta sanya su ciki. Mr. Obama yace sai tayu a siyasance wan dokar bata da farin jini,duk da haka ya yi kiraga ‘yan majalisa suyi wani abu a madadin miliyoyin Amurkawa dake fadi tashi karkashin tsarin kiwon lafiya na yanzu.

Wakilai ‘yan Jam’iyyar Republican suna ci gaba da nuna matukar adawarsu kan wan nan doka. A cikin jawabinsa na karshen mako,shugaban wakilan Republican a majalisar,John Boehner,yace idan kudurin ya zama dokar hakan zai kara kudin haraji,kuma gwamnati zata tsunduma cikin shawarwarin kiwon lafiyar jama'a.

XS
SM
MD
LG