Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Sama Sun Fara Tashi A Turai


Jiragen Sama Sun Fara Tashi A Turai

<!-- IMAGE -->

Jiragen saman kasashen Turai sun fara tashi da sauka, a bayan da hayaki da toka daga wani dutsen mai aman wuta a kasar Iceland suka mamaye samaniyar akasarin nahiyar suka hana zirga-zirgar jiragen sama.

Hukumar kula da zirga-zirgar jirage a sama ta nahiyar Turai, Eurocontrol, ta ce a yau talata ana sa ran rabin dukkan jiragen da suka saba sauka da tashi a nahiyar za su fara zirga-zirga. A yanzu jirage sun fara tashi daga filayen jiragen Paris (Faransa) da Madrid (Spain) da Switzerland da Amsterdam (Netherlands) da kuma Frankfurt a kasar Jamus.

Amma har yanzu jirage ba su iya tashi daga kasar Britaniya a saboda tokar da ta tuttudo ta doshi kasar. Britaniya ta tura wasu jiragen ruwan yaki guda uku domin dauko 'yan kasarta da suka makale a doron nahiyar Turai.

Kwamishinan sufuri na Tarayyar Turai, Slim Kallas, yace hasashe na baya-bayan nan da masana yanayi suka bayar ya nuna cewa hayaki da tokar zasu mamaye samaniyar rabin kasashen Tarayyar Turai ne a yau talata.

Ofishin nazarin yanayin kasa na Iceland yace dutsen ya riga ya amaye kusan dukkan abubuwan dake tumbinsa a yanzu, abinda ek nufin cewa yawan toka dake fitowa yana raguwa, kuma motsin da wannan dutse keyi ya shiga wani sabon matakin.

XS
SM
MD
LG