Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Umaru Musa Yaradua Ya Koma Gida Najeriya


Shugaba Umaru Musa ‘Yar Adu’a ya koma gida Nigeria bayan jiyyar da yayi ta watanni uku a Asibitin Saudi Arebiya.Jiragen sama biyu ne suka sauka a bangaren sauka da tashin jiragen saman shugaban kasa dake birnin Tarayya na Abuja da misalin karfe ukun daren jiya Talata.

Shaidun gani da ido a filin sun tabbatar da ganin an dauki ‘yar Adu’a a cikin motar daukan maras lafiya (Ambulans)aka fice dashi daga filin jirgin saman, amma ba’a tantance inda aka kaishi ba. Shugaba ‘Yar Adu’a na fama daciwon zucciya ne, kuma tafiyarsa asibtin Jidda domin jiyya, hakan ya janyo matsalar cece-kucen siyasa da yiwa kundin tsarin mulkin Nigeria hawan kawara.

Majalisar dokokin Nigeria ta kada kuri’ar amincewa mataikaminsa Goodluck Jonathan zama mukaddashin shugaban kasa a tsahon lokacin da yake kwance a Asibtin Saudi Arebiya.

XS
SM
MD
LG