Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Afghanistan Ana Aikawa da Sakonnin Yabawa 'Yan Jarida Da Kungiyar Taliban Ta Kashe


Mayakan Taliban

Har zuwa jiya Lahadi ana ta samun sakonnin yabawa jaruman 'yan jarida David Gilkey da Zabihullah Tammana wani ba'amarike da tafintansa dan Afghanistan da kungiyar Taliban ta kashe ranar Lahadi yayinda aka harbesu da roka.

Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani yayi allawadai da kisan da aka yiwa 'yan jaridan a shafinsa na Twitter inda yace kashe Tammana da Gilkey hali ne irin na matsorata.

Ofishin jakadancin Amurka a Kabul, babban birnin Afghanistan, da Janar John Nicholson, kwamandan kawancen NATO sun mika gaisuwar ta'aziya. Haka ma sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry, shi ma ya mika sakon ta'aziya tare da cewa 'yan jaridan gwarzayen ma'aikata ne.

Gilkey da Tammana an kashe su ne da sojojin Afghanistan biyu yayinda da suke tafiya cikin wata mota da ta fada cikin ruwan harsashen Taliban da rokoki jim kadan bayan sun wuce wani sansanin soja dake garin Helma cikin yankin Marjah. Garin da kauyukan dake kewaye dashi wuri ne da 'yan Taliban suka fi karfi kuma nan ne cibiyar sarafa hodar iblis, hodar dake basu makudan kudi.

Gilkey dan shekaru hamsin da haihuwa yana yiwa wani gidan rediyon Amurka da ake kira National Public Radio, ko NPR a takaice, aiki ne. Ya taba samun lambar yabo akan hotuna da bidiyo masu fadakarwa. Rediyon NPR yace shi ne dan jarida na farko da ya shiga kasar Afghanistan ba tare da rakiyar jami'in tsaro ba tun ranar 11 ga watan Satumbar 2001 lokacin da 'yan ta'ada suka kai wa Amurka hari.

XS
SM
MD
LG