Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Amurka Likitoci a jihar Massachusetts Sun Samu Nasarar Dasawa Wani Zakari


Wasu cikin likitocin da suka dasawa Thomas Manning zakari
Wasu cikin likitocin da suka dasawa Thomas Manning zakari

Kodayake shekaru goma da suka gabata likitoci a kasar China sun yi kokarin dasawa wani zakari amma basu ci nasara ba amma a karon farko a Amurka likitocinta sun samu nasarar dasawa wani zakari tare da kyautata zaton zai warke sumul

Wani mutum a jihar Massachusetts yana samun jiya yanzu a wani asibiti dake birnin Boston sanadiyar zakari da likitoci suka dasa mashi.

Mutumin Thomas Manning dan shekaru sittin da hudu ya rasa zakarinsa ne saboda kamuwa da cutar daji da ya kamu da ita a shekarar 2012. Tun daga lokacin sai makon jiya aka bashi kyautar wata ta wani likita da ya rasu. Likitan ya bada zakarinsa kafin ya rasu domin a dasawa Thomas Manning. To saidai ba'a bayyana sunan likitan ba bisa ga bahasin da ya bari kafin ya rasu.

Manning yace yana son jama'a su ji labarin dashen da aka yi masa wanda ya dauki likitoci sa'o'i 15 kafin su kammala saboda wasu dake cikin irin yanayinsa su samu karfafawa su kawar da jin kunya domin sun rasa zakarinsu.

Idan abubuwa sun tafi daidai likitoci suka ce Manning zai iya yin boli kamar kowa ya kuma cigaba da rayuwa irin ta cikakken namiji. Likitocin suna son su tabbatar sun samu nasara kafin su sake yiwa wani irin wannan aikin tiyatan ma wasu da suka hada da sojojin da suka ji rauni.

A kasar Afirka Ta Kudu likitoci suka taba dasawa wani zakari bara wanda kuma ya yi nasara ya kuma kasance irinsa na farko a duk fadin duniya.

Shekaru goma da suka wuce an taba kokarin yin hakan a China amma ba'a ci nasara ba. Mutumin ya gayawa likitoci su cire zakarin da suka dasa masa saboda shi da matarsa zuciyarsu bata kwanta ba da dashen.

Likitan da ya jagoranci likitoci 50 akan wannan aikin tiyatan Dr. Curtis Cetrulo na General Hospital Boston yace Thomas Manning yana son ya warke ya cigaba da rayuwarsa kaman kowa.

XS
SM
MD
LG