Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Amurka Wani Tsohon Gwamna da Matarsa na Fuskantar Daurin Shekara 30 Sabili da Cin Hanci


Tsohon Gwamnan Virginia Gov. Bob McDonnell da matarsa Maureen.

Wata kotu a Amurka ta samu tsohon gwamnan jihar Virginia da matarsa da laifin cin hanci da rashawa.

Wani tsohon Gwamnan jihar Virginia dake nan Amurka da matarsa suna fuskantar zaman fursina na lokaci mai tsawo bayanda masu taimakawa alkali yanke shari’a, jiya Alhamis, suka same su da lafiin karbar cin hanci daga hanun wani dan kasuwa.

Kotu ta same tsohon gwamna Bob Mcdonnell da laifuffuka daban daban 11 na cin hanci d a rashawa, bayanda ya karbi basussuka da kyaututtukan sutura, da daukar nauyin tafiye tafiyensa, shi kuma ya dauki alkawarin zai taimakawa kamfanin sayarda magungunan karawa jiki kuzari ya saida hajarsa ajihar. Matarsa kuma an sameta da laifuffuka tara shigen na mijinta.

Da tauraruwarsa ta haska a jam’iyyar Republican, lokacinda yayi gwamnan jihar Virginia daga shekara ta 2010 har zuwa watan janairun bana lokacinda msu gabatar da kara suka gabatar da tuhuma akansa.

Tsohon gwamnan da maidakinsa sun karbi kudi da kaya na dala dubu 177, kamar kusan Naira milyan 28 da rabi daga hanun dan kasuwar mai suna Jonnie Williams.

Sai cikin watan janairun badi ne alkali zai zartas da yawan shekarun da zasu yi a gidan kaso. Tsohon gwamnan da mai dakinsa suna fuskantar zaman fursina na kusan shekaru 30.

XS
SM
MD
LG