A shirin A Bari ya Huce na wannan makon mun baku labarin Bafullatani da Tela wanda tela ya boye a bayan kyaure yace a gayawa Bafullatanin yayi tafiya don bai cika alkawarin kammala dinki da aka bashi ba. Da Bafullatani ya isa aka gaya mashi ya kuma duba kasa yaga kafar telan a bayan kyaure sai yace a gayawa telan idan zai yi tafiya kada ya rika barin kafarshi a baya.
Shi kuwa Babarbare bayan ya karbi sabon dinkinshi a wurin tela ya zuba sutura ya tafi kasuwa. Bayan ya shiga jama'a ya sami wuri zai zauna sai wando ya kece. Haushi ya kama shi ya tashi bai tsaya ko ina ba sai wurin tela. ya tsaya a bakin kyaure yace a kira mashi tela waje, ya tambaye shi, "wandon da ka dinka min na zama ne ko kuma na tsayawa". Da telan ya fahimci abinda ya faru sai yace, na tsayuwa ne. Sai Babarbare yace, "ka yi sa'a. Nan gaba idan na kawo maka dinki ka yi mani na zama".
A cikin wadannan mutanen biyu wanene yafi baku dariya>
Facebook Forum