Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Bari Ya Huce: Labarin Bafullatana Da Ta Ga Kanta A Madubi Ta Zaci Kishiya Ce- Yuli 04, 2020


Alheri Grace Abdu

A wannan shirin, Ali Na Mailaya wani ba'are a Jamhuriyar Nijar ya maida martani bisa labarin da aka bada makon jiya.

Na Ali ya bada labarin wata Bafullatana da mijinta ya sayo mata tsarabar madubi, da yake wannan ne karon farko da ta duba madubi,da ta ga kanta a ciki ta zaci mijinta ne ya yi mata kishiya sai ta yi yaji ta tafi da madubin gida da nufin nunawa iyayenta amaryar da take tunanin mijinta zai auro. Ko da ta mikawa mahaifiyarta madubin ita ma ta ga kanta a ciki sai ta ce, " ca nike ma wata kyakkyawar budurwa ya samo da ta fi ki kyau yake so ya aura, ashe tsohuwa ce" ba ta san cewa kanta take kallo a madubin ba.

Saurari cikakken shirin:

Labarin Bafullatana da madubi:29:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:29:49 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG