Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A BARI YA HUCE: Labarin Bafullatani Da Likita, Maris 20, 2021


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Wani bafulatani ne ba shi da lafiya sai aka bashi shawara ya tafi asibiti. Da ya ke ya saba gani likitoci su na ce wa a kai bayan gida ko fitsari ko kuma a debi jini a gwada, sai ya nemi sabuwar robar lemun Lacasera ya cika da fitsari ya tafi da shi asibiti. Da shigarsa wurin likita sai ya mika mashi kwalbar ya ce wa likitan ya sha ya ji ko da zaki. Likita kuwa cikin wasa ya karbi kwalbar Lacasera ya kurba, sai ya cewa Bafullatani, babi zaki ko ka kara ruwa a lemun ne? Sai bafulatanin nan ya ce a’a, nima tsintar robar na yi kan hanya shine na yi fitsari ciki na kawo ka sha ka ji ko ina da ciwon suga, tun da ba zaki ya nuna ba ni da ciwon suga ke nan.

Saurari cikakken shirin:

A Bari Ya Huce: Labarin Dan Fulani Da Likita-24: 00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:24:24 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG