Bayan barayi sun gama binciken mutanen da ke cikin mota sai suka ce "ina da ke zaune nan?" Sai fasinja suka ce dan fulani ne kuma ya gudu. Sai shugaban barayin ya ce in dai dan fulanin asali ne zai zo hannu, ya umarci barayin su shiga jeji su kira sau uku zai fito.
Barayin suka shiga jeji suna kiran Bafullatani, bayan sun kira shi sau uku bai amsa ba, sai kuma koma suka cewa shugabansu wanda yake zaune karkashin wata bishiya cewa, su hakura kawai Fulani ya tsare, ashe dan fulani na saman bishiya yana kallon su, sai gogan naku ya ce "ba sau uku kuka kira ni ba Aradun Allah ko sau dubu za ku kira ni ba zan fito ba.
Saurari cikakken shirin ka sha dariya.
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.