Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Binciki Kalamun da Shugaban Philippines Yayi - MDD


Shugaban Philippines Rodrigo Duterte

Shugaban Cibiyar Kare hakkin Bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ya yi kira da a binciki kalaman da shugaban Philippines Rodrigo Duterte yayi, inda da bakinsa yake fadar cewa ya taba kashe wasu da ake zargi da aikata laifukka.

Kwamishinan cibiyar kare hakkin bil adama ta MDD din, Zeid Ra’ad ya yi kira ga hukumomi a Philippines da su kaddamar da gagarumin bincike a kan maganar kisa da shugaba Duterte ya yi a ranar Juma’a inda yace ya harbe kuma ya kashe akalla mutane uku a lokacin da yake rike da mukamin magajin garin Davao.

Zeid yace wani abin al’ajabi ne ace akwai wani tsarin shara’a da ba zai himmatu wajen gudanarda bincike da kuma shirya daukan matakan shara’a akan duk wani da ya fito, da bakinsa, yace ya kashe wani ko wasu ba.

Duterte ya fada a cikin jawabansa a kwana kwanannan cewa a can baya, lokacin yana magajin garin na Davao, ya sha zagaya garin akan babur yana neman bata-gari, yana kuma kashesu don yan sanda su yi koyi da shi.

Sakataren Gwamnatin kasar Amurka Michael R. Pompeo

Magoya Bayan Trump Sun Afkawa Ginin Majalisun Amurka

Magoya Bayan Shugaba Donald Trump Sun Mamaye Ginin Majalisar Dokokin Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:56 0:00

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni
XS
SM
MD
LG