Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Amurka Bata Tuntubi Kasar Philippines Ba Kan Barazanar Da Tayi


Philippines Duterte US
Philippines Duterte US

Fadar Shugaban Amurka ta White House ta ce har yanzu bata tuntubi gwamnatin Philippines akan barazanar da Philippines din tayi ba, na cewa tana neman yanke huldan harakokin soja dake tsakanin kasashen biyu.

Sanarwan ta fadar White House ta zo ne a ranar da shugaban na Philippines Rodrigo Duterte ya sake barazanar cewa zai yanke wannan huldar da Amurka, wanda wannan shine karo na biyu cikin kwannaki biyu da yake irin wannan tada jijiyar.

Duterte ya yi wannan huruci ne a babban birnin Japan, Tokyo, inda yake ziyarar aiki ta kwanaki uku. Yace yana son ya raba Philippines da sojojin kasashen waje a cikin wa’adin shekaru biyu masu zuwa nan gaba, koda kuwa ta kama ya sake nazari ko ma bata wasu yarjeniyoyin da kasar shi ta kulla da wasu kasashe.

Akwai dai sojoji Amurka yan kalilan dake a tsibirin Mindanao dake kudancin kasar ta Philippines da aka girke don su taimaka wajen yaki da masu akidar ta’addanci na Islama dake kasar.

XS
SM
MD
LG