Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Brazil Kwamitin Da'aNa Majalisar Dokoki Ya Fara Jin Bahasin Kakakinta da Aka Dakatar


Kakakin Majalisar Dokokin BrazilEduardo Cunha, wanda aka dakatar bisa zargin boye kudade a kasar waje

Kakakin majalisar dokokin kasar Brazil da aka dakatar daga bakin aiki bisa ga zargin almundahana da boye kudade a kasashen waje ya bayyana gaban kwamitin dake bincikarsa

A Brazil, kwamitin da'a na majalisar wakilan kasar, ya fara sauraron bahasi kan kakakin majalisar dokokin kasar Eduardo Cunha, wanda aka dakatar daga bakin aiki, kan zargin cewa, ya boye miliyoyin dala a wasu bankuna a kasashen ketare.

A farkon wannan wata ne aka dakatar da kakakin majalisar, bayan da kotun kolin kasar ta yanke hukunci akansa, saboda haka zaman da kwamitin majalisar yake yi,shine na duba ko a kori kakakin daga majalisar baki daya.

Cunha, yana fuskantar zargin cin hanci da rashawa, da kuma neman hana shari'a tayi aikinta,sakamkon zargin ya shirga karya ga majalisar cewa ya boye kudade a wasu bankunan a Switzeland. Duk da haka ya sake karyata wannan zargi ko a jiya Alhamis.

XS
SM
MD
LG