Accessibility links

Mahukuntan Nijar Sun Mika Wa Libya Dan Tsohon Shugaba Gaddafi


Sa'ad Gaddafi a gidan kaso a birni Tripoli bayan da aka mika shi ga hukumar kasar Libya.

An damka dan tsohon shugaban kasar Libya Sa'adi Gadaffi ga mahumkutar kasar Libya a jiya da dare an kuma tasa keyarsa zuwa gidan kaso.

A daren jiya ne mahukumtan kasar Nijer suka damka dan tsohon shugaban kasar Libya Sa'adi Gadaffi hannun mahukumtan kasar Libya dake neman sa ruwa a jallo.

A karshen watan satumba 2011 ne dai wata tawagar kasar Libya ta tsere daga kasar tdomin samu mafaka a kasar Nijer a yayin farmakin da kasashen duniya suka kaiwa kasar Libya domin murkushe niyar Canal Gadaffi,dake neman karewa da fararen hula dake zanga-zangar juyin-juya hali a kasar.

Wanna ya biyo bayan mika Janaral Abdulla Mansur babban jami'in leken asiri na kasar Libya karkashen mulkin Canal Gadaffi da aka yi a watan da ya shige.

Kuma har yanzu kasar Nijer bata ce komai ba dangane da daukan wanna mataki na mika dan na Gadaffi ga kasar.

XS
SM
MD
LG